Hizba za ta aurar da mata har da Kiristoci

Image caption Wasu daga cikin matan da aka aurar

Hukumar Hizba ta jihar Kano dake arewacin Najeriya ta ce ta fara wani sabon shiri na aurar da mata har da wasu mabiya addinin Kirista.

Darakta Janar na hukumar ta Hizba, Malam Abba Saidu Sufi ya shaidawa BBC cewa, a wannan zagayen za su aurar da mata 1,111 wadanda daga cikinsu hamsin mabiya addinin Kirista ne.

A cewar hukumar ta Hizba, nan ba da jimawa ba za a gudanar da binciken aurar da matan, kuma kwamandojinta na kananan hukumomi sun fara shirye-shiryen zabo wadanda za a aurar.

Tun a watan Mayun shekara ta 2012 ne, aka fara aurar da 'yan mata da zaurawa a jihar Kano, kuma kawo yanzu an aurar da mata fiye da dubu daya da dari uku.

Gwamnatin jihar Kano ce ke daukar nauyin auren, a yayin da masu hannu da shuni kan tallafawa ma'auratan.

Karin bayani