'Ana matukar cin hanci a Liberia'

Image caption Shugabar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf

Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch mai hedkwatarta a New York ta ce yadda cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a kasar Liberia yana kawowa kasar cikas wajen samun ci gaba tare da tauyewa 'yan kasar hakkinsu na samun adalci.

Kungiyar ta zargi 'yan sandan kasar da karbar na goro daga hannun wadanda ake zargi da aikata laifuffuka da kuma karbe kayayyaki daga hannun masu tallace-tallace a kan tituna.

Shekaru goma bayan an kawo karshen yakin basasar Liberia, har yanzu kasar na fuskantar tashin hankali da kuma aikata laifuka a kan tituna.

Kungiyar ta Human Rights watch kuma ta yi kakkkausar suka a kan 'yan sanda wadanda ta kira 'No Money No Justice' wato 'In Ba kudi - Ba adalci'.

Karin bayani