'Yan tawayen Mali da Algeria sun hade

Image caption Belmokhtar ya ce za su murkushe Faransa

Kungiyar masu tayar da kayar baya da dan kasar Algeria, Mokhtar Belmokhtar, ke jagoranta ta ce ta hade da wata kungiyar da niyyar kai hare-haren ramuwar gayya kan Faransa saboda yakin da ta jagoranta a Mali.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar mai suna Masked Men Brigade, a turance da takwararta ta kasar Mali da ake kira, Mujao, sun kafa kungiyar mai suna Al-Murabitoun.

A watan Yuli, Amurka ta ce za ta bayar da ladan dala miliyan biyar ga duk wanda ya kamo mata Belmokhtar.

Ana zarginsa da kitsa kai mummunan farmaki a masana'antar sarrafa sinadarin uranium da ke Algeria a watan Janairu.

Amurka tana tuhumarsa da laifin yin garkuwa da mutane da sace su da kuma hada baki domin yin amfani da makaman kare-dangi.

Amurkawa guda uku na cikin mutane 37 da aka kashe lokacin da dakarun Algeria suka kai farmaki a masana'antar Tigantourine domin kawo karshen garkuwar da masu tayar da kayar baya suka yi da su.

A watan Mayu, kungiyar Mujao da kuma kungiyar da Belmokhtar ke shugabanta sun kai tagwayen hare-haren hadin gwiwa a wani barikin soja da kuma ma'aikatar hakar uranium mallakin Faransa da ke Nijar, lamarin da ya yi sanadiyar kashe mutane 25.

''Za mu murkushe Faransa''

Sanarwar da kungiyoyin suka fitar, wacce kamfanin dillancin labarai na Mauritania ya wallafa ta ce,'' 'Yan uwanku na kungiyar Mujao da Al-Mulathameen sun sanar da cewa sun hade waje guda, inda suka kafa kungiya mai suna Al-Murabitoun da zummar hada kan musulmi domin cimma manufa guda daga kogin Nilu zuwa kogin Atlantika''.

Sanarwar ta kara da cewa masu fafutuka a yankin sun kara karfi kuma za su murkushe Faransa da abokanta.

A watan Janairu ne dai Faransa ta jagoranci wadansu kasashe wajen kai hari domin sake kwace arewacin Mali daga hannun 'yan tawaye, wadanda suka mulki yankin har kusan watanni takwas sakamakon rikicin da ya auku bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.

Karin bayani