Mubarak zai fuskanci daurin talala

Image caption Hosni Mubarak na fuskantar barazanar daurin talala

Sojojin Masar sun ba da izinin ayi wa tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak daurin talala, hakan ya biyo bayan sa ran da ake yi za a sallame shi daga gidan kaso cikin makon nan.

A ranar laraba ne kotun da ke sauraren karar cin hanci da rashawa ta bada izinin sallamar Mr Mubarak; cewa ya cika tsahon lokacin da zai iya kasancewa a tsare kafin a yi masa shari'a.

Lauyoyin Mr Mobarak sun ce mai yiwuwa a sallame shi daga kurkuku a yau Alhamis.

Mai shekaru 85 a duniya, Mubarak zai kara fuskantar shari'a bisa zargin hannu a kisan masu zanga-zanga, lokacin boren da ya kai ga hambarar da gwamnatinsa a shekara ta 2011.

Karin bayani