An rantsar da Mugabe a karo na bakwai

Image caption Robert Mugabe

An rantsar da Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe a karo na bakwai a matsayin shugaban kasa.

An ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar hutu a kasar, don baiwa magoya bayan Mista Mugabe dan shekaru tamanin da tara, damar halartar bikin rantsarwar da za aka yi a filin wasa na Harare.

An jinkirta rantsar da shi ne sakamakon karar da abokin hamayyarsa Morgan Tsvangirai ya shigar, a kan cewa an yi magudi a lokacin zaben.

Amma kotun tsarin mulkin Kasar ta kori karar, inda ta ce an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.

Mista Mugabe ne Pirayi Minista na farko a kasar, bayan samu 'yancin kan kasar a shekarar 1980, kuma tun daga lokacin shi ke jan ragamar kasar.

Karin bayani