Moden Lumana ta fita daga gwamnatin Nijar

Image caption Shugaba Muhammadou Issoufou

A Jamhuriyar Nijar, jam'iyyar Moden Lumana Afrika ta Shugaban Majalisar dokokin kasar Malam Hama Amadu ta sanar da matakin fice wa daga kawancen jam'iyun siyasa na MRN mai mulki.

Jam'iyyar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan wani taron gaggawa da kwamitin kolinta ya yi.

Tun a makon daya gabata ne jam'iyyar Moden Lumana ta umurci ministocinta 7 su kaurace ma gwamnatin Shugaba Muhammadou Isoufou.

Harkokin siyasa a Nijar sun dauki sabon salo ne bayan da Shugaba Isoufou ya dauki matakin kafa gwamnatin hada kan kasa, abinda ya bashi damar nada 'yan adawa a cikin gwamnatin wato 'yan jam'iyyar adawa ta MNSD nasara.

Karin bayani