Shekau: Matsayin kwamitin sulhu

Image caption Sanarwar mutuwar Shekau na kara bayyana ra'ayoyi mabambanta

A karon farko kwamitin nan da shugaban Najeriya ya kafa domin sasantawa da 'ya'yan kungiyar Jama'atu Ahlil Sunnah Lid-da'awati Wal jihad da aka fi sani da suna Boko Haram, ya bayyana yadda yake kallon sanarwar da aka bayar kan mutuwar shugaban Bokok Haram Abubakar Shekau.

Rundunar Tsaro ta Hadin Gwiwa dake aiki a jihar Borno ce ta bayar, da sanarwar cewa mai yiwuwa an kashe shugaban kungiyar, Imam Abubakar Shekau, a farkon wannan wata sakamakon wata musayar wuta da dakarun tsaro.

Jami'an tsaron dai sun ce Imam Shekau ya cika ne a wani asibiti dake Jamhuriyar Kamaru dab da kan iyaka da Najeriya inda ya je jinyar raunukan harbin bindiga da ya samu.

Mutane da dama har da masu sharhi kan harkokin tsaro sun nuna shakku kan gaskiyar labarin musamman ganin ba a nuna gawarsa ba.

Karin bayani