Uganda ta hana tusa keyar Joel Matabazi

Image caption Uganda ta bi dokar hana mika 'yan gudun hijira a tusa keyarsu

Gwamnatin Uganda da ofishinta da ke kula da 'yan gudun hijira sun hana tursasa tusa keyar tsohon mamba a cikin dogaran fadar shugaban kasar Rwanda.

Gwamnatin ta ce kama shi ya sabawa dokokin kasa da kasa kan kare 'yan gudun hijira wanda kasar Uganda na daga cikin kasashen da suka rattaba hannu.

Ministan dake kula da 'yan gudun hijira ya ce dan gudun hijira na ribatar kariyar kasa da kasa.

Joel Matabazi wanda yake kasar Uganda shekaru biyu tun bayan tserewa da ya yi daga Rwanda ana zaton 'yan sandan Uganda sun kama shi a daren Talata bisa muradin takwarorin su na Rwanda.

Karin bayani