'Yan adawa sun gana da Shugaban Ghana

Image caption Shugaba John Mahama na Ghana ya tattauna da 'yan takarar Jam'iyyun adawa

'Yan takarar neman shugabancin kasa na wasu jam'iyyun siyasar kasar Ghana a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekara ta 2012 su shida sun gana da shugaba John Mahama.

Ganawar dai anyi ta ne da nufin shawo kansu, su tabbatar an samu zaman lafiya a kasar.

Haduwar da 'yan takarar Jami'yyun adawar suka yi da shugaban kasar Ghana, ta zo ne a dai-dai lokacin da ake zaman dar-dar ana dakon hukuncin karar da babbar jam'iyyar adawar kasar wato NPP ta shigar, inda take kalubalantar sahihancin zaben shugaba John Mahama da akayi a bara.

An ambato shugaban John Mahama na cewa dimokradiyyar Ghana za ta ci gaba da dorewa ko ya ya kuwa hukuncin kotun ya kasance.

Karin bayani