Ana shirin aurar da mata 1000 a Kano

Image caption An sake daurar aniyar auren mata 1000 a Kano

Hukumomi a Najeriya sun fara wani sabon shiri na sake aurar da mata sama da dubu daya a birnin Kano dake arewacin kasar.

Tuni dai hukumar tabbatar da aiki da shari'ar musulunci ta Hizba a Jihar Kano wadda ke jagorantar auren ta sanar da kwamandojin ta na kananan hukumomi su fara shirye shiryen zabo wadan da za a aurar.

Hukumar ta ce a wannan karon za a hada da wasu mabiya addinin kirista a tsarin auren da hukumar ta Hizba take shiryawa.

Kawo yanzu dai hukumar ta aurar da mata dubu daya da dari uku da hamsin a jerin auren da aka yi har sau uku a Jihar tun lokacin da aka fara shirin.

Karin bayani