Sojin Najeriya na kara dabaru kan tsaro

Image caption Sojin Najeriya na bita kan tsaro a kasar

A Najeriya Sojojin kasar na sake daura damarar yaki da tabarbarewar tsaro yankuna arewa maso gabas da kuma wasu sassa na arewa maso yammacin kasar.

Dakarun dai an umarce su da hadin kai a tsakaninsu da takwarorinsu a wani matsayi da aka dauka ta hanyar cimma burin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa.

Wannan dai na cikin abubuwan da taron kwamandoji na biyu na sojojin Najeriya dake aiki a Arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas ya duba.

An gudanar da taron ne a Kaduna domin kara zaburar da dakarun dake neman tabbatar da zaman lafiya a wasu yankuna na kasar da ake fama da tada kayar baya.

Karin bayani