'Yara miliyan 1 sun yi gudun hijira a Syria'

Yara 'yan gudun hijira na Syria
Image caption 'Yan gudun hijira a Syria na karuwa har da kananan yara

Wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a ranar Juma'a ya ce, a yayin da fadan Syria ya shiga shekara ta uku, yaran kasar da suka yi gudun hijira sun kai miliyan daya.

Rahoton wanda hukumomin majalisar guda biyu watau mai kula da 'yan gudun hijira UNHCR da kuma mai kula da tallafawa kananan yara UNICEF ya ce yaran sun kai rabin adadin mutanen da suka yi gudun hijira daga Syria.

Galibin yaran sun tafi gudun hijiran ne zuwa kasashen Turkiyya da Jordan da Lebanon da kuma Masar.

Wasu kuma na dada nausawa zuwa kasashen yammacin Afrika da kuma Nahiyar turai.

Rahoton ya nuna cewa yara dubu dari bakwai da arba'in da suka yi gudun hijirar 'yan kasa da shekaru goma sha daya ne.

Karin bayani