'Cin hanci ya zama ruwan dare a Liberia'

Image caption Cinhanci a Laberia na shafar ci gaban kasar

Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch mai hedikwatarta a New York, ta ce cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a Liberia.

Cin hancin inji Hukumar ya tumbatsa yadda ya kai munzalin kawo wa kasar cikas wajen samun ci gaba.

Haka kuma yana kuma tauye wa 'yan kasar hakkinsu na samun adalci.

Kungiyar ta zargi 'yan sandan kasar da karbar na goro daga hannun wadanda ake zargi da aikata laifuffuka da kuma karbe kayayyaki daga hannun masu tallace tallace akan tituna.

Karin bayani