Kotu ta samu shaidu akan Bo Xilai.

Bo Xilai a rana ta hudu a cikin kotu.
Image caption Kotu ta gama tattara shaidu game da shari'ar ad ake yi wa Bo Xilai

Kotun da ke sauraren karar fitaccen dan siyasar kasar China Bo Xilai da laifin cin hanci da kuma yin amfani da ikon da aka ba sa ba bisa ka'ida ba a birnin Jinan.

Ta sanar a shafin ta na yanar gizo cewa an gama tattara shaidu akan shari'ar.

A rana ta hudu na zaman kotun Mr Bo Xilai ya yi kokarin kare kansa, game da zargin da wani jami'in 'yan sanda ya masa na yin katsalandan game da batun kisan da maidakinsa ta aikata.

Wakilin BBC ya ce masu sanya ido sun yi matukar mamaki da shari'ar ta kai har tsahon kwanaki hudu.

A da su na tsammanin ba za a dauki lokaci ana yin shari'ar ba.

Karin bayani