Mandela yana ci gaba da murmurewa

Gwamnatin Afurka ta kudu ta ce, tsohon shugaban kasar Nelson Mandela yana ci gaba da kasancewa a cikin wani hali, amma wasu lokuttan yana samun sauƙi.

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar Afurka ta kudun ta ce, Mandela yana ci gaba da nuna karfin hali, kuma yana samun sauki sakamakon irin kulawar da yake samu daga likitoci.

Nelson Mandela wanda ya jagoranci yaƙi da wariyar launin fata yana asibiti tun daga watan Yuni sakamakon cutar huhu da yake fama da ita.