Angela Kane ta isa Syria kan binciken makamai

Angela Kane, wakiliyar Majalisar Dinikin Duniya
Image caption Angela Kane, wakiliyar Majalisar Dinikin Duniya

Babbar jami'ar majalisar dinkin duniya mai sa ido a kan kawar da makamai, Angela Kane ta isa birnin Damascus domin matsa lamba ga gwamnatin Syria ta baiwa masu binciken makamai damar kaiwa ga wuraren da ake zargin an kai hari da makamai masu guba.

Ana dai zargin gwamnatin Syrian ne da amfani da makamai masu guba akan mazauna garin Ghauta, amma gwamnatin Syrian ta musanta wannan zargi.

Wakiliyar BBC ta ce, yayin da gwamnatin Syria ke cigaba da fuskantar matsin lamba ta fuskar diplomasiyya, tana kuma fuskantar barazanar matakin soja daga Amurka.

Sai dai kuma gidan talabijin na gwamnatin Syria ya ce, soja da suka shiga yankunan dake karkashin 'yan tawaye sun samu alamun guba.