Ana ci gaba da shari'ar Bo Xilai

Image caption Bo Xilai na fuskantar shari'a

A ci gaba da shari'ar da ake yi wa wani kusa a shugabancin China, Bo Xilai, shari'ar da ake sa ido sosai a kanta, an saurari bahasi akan kisan dan kasuwar nan dan Birtaniya, Neil Heywood.

An dai yankewa mai-dakin Bo Xilai, wato Gu Kailai hukuncin kisan da aka jingine, dangane da kisan dan kasuwar.

Ana dai zargin Mista Bo ne da aikata cin hanci da rashawa da kuma yin amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba, amma ya musanta zargin.