Mugabe ya gargadi Amurka da Burtaniya

Robert Mugabe
Image caption Shugabbin Kasashen kudancin Amurka sun nemi a dagewa Zimbabwe takunkumi

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya gargadi Amurka da Burtaniya dasu dage takunkumin da suka sanyawa Kasar sa, ko kuma yace su fuskanci ramuwa.

Shugaban ya ce lokaci zai zo da zaiyi amfani da matakan ramuwar gayya akan kamfanoni mallakar Kasashen waje wadanda su suka fi yawa a kasuwar hannayen jarin Zimbabwen.

Mr. Mugabe dai ya kasance akan karagar mulki shekaru talatin da uku yanzu haka, ya kuma sake lashe zaben da akai takaddama akansa a watan daya gabata.

Ya yi wadannan kalamai ne a wajen jana'izar wani jami'in rundunar sojin saman Kasar

Mako guda daya wuce ne dai Shugabannin Kasashen kudancin Afirka suka ce ya kamata a dage duk wani takunkumi da aka kakabawa Kasar bayan abinda suka kira sahihin zaben da aka gudanar a Kasar kuma cikin lumana.

Karin bayani