Wani yaro yayi fedar jirgin sama a Nijeriya

Wani jirgin saman Nijeriya
Image caption Wani jirgin saman Nijeriya

A Nijeriya wani yaro mai suna Daniel Ikhehina, ya tsallake rijiya da baya, bayan da ya buya cikin tayar jirgin sama aka yi tafiyar kusan rabin awa da shi a jirgin sama daga filin jirgin saman Benin na jihar Edo, zuwa Lagos.

Sai bayan da jirgin saman ya sauka a Lagos ne aka ga yaron mai shekaru sha hudu, ya fito daga inda ya buya, a kurumbon tayar jirgin saman, mallakin kampanin Arik Air.

Mr Yakubu Dati, kakakin ma'aikatun zirga zirgar jiragen saman Nijeriya , ya tabbatar masa da BBC aukuwar lamarin, ya kuma ce suna gudanar da bincike.

Ya ce hakan ba yana nufin akwai sakaci ba ne a matakan tsaron da suke dauka.