Gwamna Suntai ya isa Jalingo

Image caption Gwamna Suntai yayin da ya iso Abuja

Rahotanni daga Nijeriya na cewa a dazu ne gwamna Danbaba Suntai na jihar Taraba ya koma gida Nijeriya kuma har ya isa Jalingo bayan jinyar da ya shafe kimanin watanni goma yana yi a ƙasashen waje.

Gwamna Danbaba Suntai ya sauka a Abuja ne daga Amurka, daya daga cikin wuraren da yayi zaman jinya bayan hadarin jirgin saman da yayi.

Farfesa Jerry Gana na daga cikin wadanda suka tari gwamnan.

A kwanakin baya dai an yi ta muhawara kan ko yana da cikakkiyar lafiyar da zai iya komawa kan kujerar mulki, inda wasu ke kiran da a rantsar da Alhaji Umar Garba, mukaddashin gwamnan jihar a matsayin gwamna.