An fara binciken makamai masu guba

John Kerry, Sakataren Harkokin wajen Amurka
Image caption John Kerry, Sakataren Harkokin wajen Amurka

Sakataren Harkokin wajen Amurka, John Kerry ya yi kakkausan tir da abinda ya kira amfani da makamai masu guban da ba za a iya musantawa da gwamnatin Syria ta yi ba.

Da yake magana a Washington Mr Kerry ya ce Shugaba Obama ya yi amannar cewar dole ne a riki Syria da alhakin yin amfani da makaman da suka fi muni a kan mutanen da suka fi rauni.

Ya kara da cewar Shugaban zai yanke shawara a cikin kwanaki masu zuwa game da irin matakan gaba da za a dauka.

Mr Kerry ya ce dole ne duniya ta mike don tabbatar da cewar ba a kara amfani da makaman masu guba ba.

Tun farko masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun je gurin da aka yi zargin an kai hari da makamai masu guba a Syria.

Wani faifan bidiyon da aka nuna a shafin intanet, ya nuna masu binciken na magana da mutane tare da daukar samfuri domin yin gwaji, a wajen garin Damuscus.

Kafin sannan dai wani da ba a san ko waye ba, ya harbi tagawar masu binciken makaman yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gurin, amma babu wanda ya jikkata.

A ranar Lahadi ne gwamnatin Syria ta amince ta bar masu binciken su je gurin.

Sai dai kuma gwamnatin Amurka ta ce wannan matakin ya makara, kuma ta yi nuni da cewa Shugaba Obama na duba yiwuwar kaiwa Syria harin soji.

Karin bayani