Dakarun Isra'ila sun kashe Palasdinawa

Wasu sojojin Isra'ila
Image caption Wasu sojojin Isra'ila

Dakarun Isra'ila sun kashe Palasdinawa uku, tare da jikkata wasu 14, a sansanin 'yan gudun hijira na Qalandiya dake arewacin birnin kudus.

Dakarun Isra'ila sun ce, sun kashe Palasdinawan ne, saboda kare 'yan sandan tsaron iyakarsu, da suka ce Palasdinawa sun kaiwa hari a cikin dare.

Kakakin shugaban Palasdinawa, Nabeel Abu-Rudeineh ya yi tur da kisan.

Bude wutar ya sa a soke taron tattaunawa tsakanin bagarorin biyu da yakamata a yi a Jericho a ranar Litinin.