Maza biyu za su auri mace daya a Kenya

Daya daga cikin mazajen dake son auren mace daya
Image caption Lauyoyi sun ce za a amince da auren ne a hukumance, idan mazajen sun tabbatar da cewa al'adarsu ta amince da hakan

A Kenya wasu maza biyu sun dauki matakin auren mace guda, domin warware takaddamar da ke tsakaninsu, abin da ba a saba ganin irinsa ba.

Mazan biyu sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya, da za ta ba kowannensu damar yin mu'amala da matar ba tare da shiga gonar dan'uwansa ba.

Matar, wacce bazawara ce, bayan mutuwar mijinta ta amince da tsarin, kuma a cewarta ba za ta iya rabuwa da kowanne daga cikin mazajen biyu ba.

Mazan sun yanke shawarar auren matar ne, bayan sun gano cewa kowannensu na nemanta fiye da shekaru hudu.