Jami'oi biyu ne kawai a kasar Liberia

Shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf
Image caption Liberia ta kasance kasatr da ta fara zama jamhuriya ta farko a Afrika.

Kasar Liberia na da jami'oin gwamnati biyu ne kacal, Jami'ar Liberia da ke Monrovia da sabuwar jami'a da ke kusa da iyakar Ivory Coast.

Hakan ya sa mutane ke ruguguwar samun gurbi ga 'ya'yansu, musamman a jami'ar Monrovia, saboda ba kowanne zai iya biyan kudin makaranta a makarantu masu zaman kansu ba.

Abin da ke janyo cunkoso a jami'oin, lamarin da ya sanya daukar sababbin dalibai ya zama mai wuya a 'yan shekarun nan.

Yanzu haka dai fiye da dalibai dubu 20 ne, suka yi jarrabawa domin shiga jami'a a watan gobe.