Majalisa za ta yi nazari kan wasikar Suntai

Image caption Mista Suntai dai ya samu rauni a kwakwalwarsa ne cikin wani hadarin jirgin sama a Yola.

A yau Talata ne ake sa ran 'yan majalisar dokokin jahar Taraba za su yi wani zama domin yin nazari kan wata wasika da bangaren gwamnati ya aika musu, wadda ke sanar da su cewar gwamnan jahar ya dawo bakin aiki amma zai tafi wani dogon hutu.

Majalisar dai za ta tantance idan Gwamna Danbaba Danfulani Suntai ne ya rubuta wasikar da kansa kamar yadda doka ta tanada ko kuma a'a.

Rahotanni dai sun ce an hana mataimakinsa da kuma wasu daga cikin 'yan majalisar da suka je gidan gwamnan domin duba shi ganinsa.

Gwamnan dai ya kwashe kimanin watanni goma yana jinya a kasashen Jamus da Amurka kafin a dawo da shi gida ranar Lahadi amma cikin yanayi rashin lafiya.

Karin bayani