Wani gini ya rufta da mutane uku a Abuja

Taswirar Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya
Image caption Ruftawar gini ba wani sabon abu bane a Najeriya, lamarin dake sanadiyar rayuka

A Najeriya mutane akalla uku ne aka ba da rahoton sun mutu, yayin da wasu suka jikkata bayan wani sashe na wani sabon gini da suke aiki a kai ya rufta, a Unguwar Maitama dake Abuja.

Rahotanni sun ce, leburorin sun shiga karkashin ginin ne, inda suke yanke katakai a karkashin dakin da aka zuba a ranar Litinin.

Ko da yake masu ginin da hukumomi ba su ce komai ba tukuna game da lamarin, wasu na ganin ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya a 'yan kwanakin nan ne ya zaizaye ginin.

Wakilin BBC wanda ya je inda lamarin ya auku ya ce an garzaya da mutum guda asibiti, yayin da ake dakon babbar mota domin tono sauran biyun da ginin ya rufta da su.