Kano da Nijar sun hada gwiwa a kan ilimi

Shugaban kasar Nijar, Muhamadou Issoufou
Image caption Makarantar ita ce irinta ta farko ta hadin gwiwa tsakanin hukumomi a yammacin Afrika.

Jamhuriyar Nijar da jihar Kano a Nigeria, sun fara aiwatar da wata yarjejeniya, wacce a karkashinta daliban da suka gama makarantun firamare a Kano, za su hadu da takwarorinsu na Nijar domin karatun sakandare.

Shirin dai zai gudana ne a wata makarantar Sakandare ta kwana irin ta ta farko a jamhuriyar Nijar.

Hukumomin bangarorin biyu ne dai suka dauki nauyin kafa makarantar da kuma tafi da ita.

Daliban farko da za su shiga makarantar daga Kano sun kama hanya zuwa jamhuriyar Nijar, domin karatun shekaru bakwai.