Iyalai daga Najeriya na gudun hijira a Chadi

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby
Image caption Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby

Jama'a da dama ne ke kwarara cikin kasar Chadi daga Najeriya, domin gujewa farmakin da dakarun Najeriyar ke kaiwa 'ya 'yan kungiyar nan da ake kira Boko Haram.

Daruruwan iyalan 'yan gudun hijirar sun isa garin N'Gbouboua dake kudu-maso-gabashin kasar a yankin tafkin Chadi.

Wasu cikin masu gudun hijirar dai tuni suka kama kananan sana'oi, domin samun abin sawa a baka.

Dama can dubban 'yan gudun hijira ne suka tserewa farmakin sojoji, musamman daga jihohin Borno da Yobe zuwa jamhuriyar Nijar da Kamaru.