Najeriya za ta mika Babafemi ga Amurka

Kotun daukaka kara ta Najriya
Image caption Babafemi ya gudo daga Amurka zuwa Najeriya, a lokacin da hukumomi ke yunkurin kama shi

Wata babbar kotun Najeriya dake zamanta a Abuja, ta yanke hukuncin mika Lawal Olaniyi Babafemi ga gwamnatin Amurka, bisa zargin dake da alaka da ta'addanci.

Kotun ta ce za a mika Babafemi wanda aka fi sani da Ayatollah, ga Amurkan nan da kwanaki 15.

Tun da fari a zaman kotun na yau wanda bai cika sosai ba, Babafemi ya shaida wa lauyansa cewa, ya amince a mika shi ga hukumomin Amurka.

Amurka dai na zargin Babafemi da alaka da kungiyar AlQa'ida a Yemen, kuma ya gudo Najeriya, domin taimaka wa kungiyar daukar masu magana da harshen Ingilishi aiki.