'Yan Boko Haram sun kashe mutane 20

Image caption An kai harin ne a garuruwan Bama da Damasak

Wadansu hare-hare biyu da ake zargin 'yan Kungiyar Boko Haram ne suka kai, sun yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane ashirin a jihar Bornon Najeriya.

An kai hare-haren ne a garuruwan Bama da Damasak kuma an kai su ne a kan mambobin kungiyar 'yan sintiri da aka kafa domin yaki da 'yan bindigar.

Sojojin Najeriya ne ke kafa irin wadannan kungiyoyi na 'yan sintiri domin taimaka musu a yayin da su ke farautar 'yan kungiyar Boko Haram.

Wannan farmaki da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kaddamar na da nufin kawo karshen aikace-aikacen 'yan sintirin wadanda suke taimakawa jami'ian tsaro wajen murkushe 'yan Boko Haram.

Karin bayani