Bikin tunawa da jawabin Martin Luther King

Image caption Margayi Martin Luther King

Yau laraba 28 ga watan Agusta ne ake cika shekaru hamsin da shaharraren bakar fatan Amurka, marigayi Martin Luther King, ya gabatar da jawabinsa wanda yayi fice a duniya wato " I have a dream " a lokacin wani gangami a birnin Washington na Amurka a shekarar 1963.

Gangamin wanda mutane kusan dubu dari biyu da hamsin suka halarta ya taimaka wajen shawo kan gwamnatin Amurkar daukar wasu muhimman matakai da suka hada da 'yanci ga bakaken wajen kada kuri'a da kuma zamanta kewa, matakin daya sauya fasalin Amurka.

Shekaru hudu bayan wannan jawabin, aka yi wa Martin Luther King kisan gilla abinda ya janyo zanga-zanga a fiye da birane 100 na Amurka.

Shugaba Obama zai hade da sauran mazan jiya wajen macin, tare da iyalan Dr Kings da sauran fitattun bakaken fata Amurkawa don murnar zagayowar wannan ranar.