Syria: Masu bincike za su koma aikinsu

Image caption Ana binciken ne a unguwannin Ghouta da Moadhamiya inda aka kai harin.

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya a Syria za su ci gaba da aikin da suke yi a wajen birnin Damascus yau Laraba bayan dakatawa ta kwana daya.

Suna dai ziyarar wasu wurare biyu ne inda ake tuhumar an kai hari da makamai masu guba a makon jiya; abin da ya kashe daruruwan mutane.

Masu binciken sun dakatar da aikin ne bayan da aka harbi jerin motocinsu daga boye ranar litinin sa'adda suke kokarin ziyartar wata unguwa da ke wajen Damascus; sai dai babu wanda ya samu rauni. Kasashen yamma dai na zargin sojan Syria da harba makamam masu guba, amma gwamnatin Syriar ta sha musanta hakan.

Karin bayani