Yara masu aikin zinari na iya kamuwa da cuta

Yara masu aikin hakar zinari
Image caption Wani lokacin ramukan da yaran ke aiki kan rufta, musamman a mahakar da bata da lasisi

Duban yara dake aiki a mahakar zinari a Tanzania, na fuskantar hadarin kamuwa da cuta da za ta iya kaiwa ga mutuwa.

Kungiyar kare hakin bil'dama ta Human Rights Watch ta bankado sabbin bayanai, a kan cin zarafin yara, wadanda shekarunsu ba su wuce takwas ba, dake aiki a karkashin kasa har sa'o'i 24.

Kakakin Kungiyar Janine Morna, ta ce "Yaran na shakar kura mai yawa sosai, abin da kuma kan iya shafar huhunsu. Kuma suna shakar tiririn sinadarin Mercury mai guba wajen hakar zinaren."

Kasar Tanzania dai na da doka mai tsauri da ta haramta amfani da yara a mahakar ma'adanai, amma kungiyar ta Human Rights na ganin dole ta tursasa a bi dokar.