Suntai: Kan 'yan majalisar Taraba ya rabu

Gwamnan jihar Taraba, Danbaba Dan Fulani Suntai
Image caption Rashin lafiyar Suntai ya zamo batun da jama'ar Traba ke tattauna wa a kai

Majalisar dokokin jihar Taraba ta bukaci gwamnan jihar, Danbaba Danfulani Suntai ya bayyana a gabanta, domin yi mata bayani game da lafiyarsa.

Majalisar na so ne ta tantance yadda zai iya shugabancin jihar, amma wasu daga cikin 'yan majalisar sun nuna adawarsu da hakan.

A nasu ganin wasikar da bangaren zartarwa ta mika wa majalisar dake nuna cewa ya samu sauki da zai iya ci gaba da mulki ta wadatar.

Tun bayan dawowar gwamnan jihar daga jinya a kasashen Amurka da Jamus a ranar Lahadi, kace-nacen siyasa ya karu a kan batun lafiyarsa.