'yan Syria na shirya wa fuskatar hari

Image caption Masu goyon bayan gwamnati nakunna wakokin yabon Shugaba Assad da kuma yiwa wurare fenti da launukkan tutar kasar.

Mazauna Damascus babban birnin kasar Syria sun fara shirya wa fuskantar hare-hare ta sama da Amurka ka iya kaiwa kowane lokaci.

Rahotanni sun ce mutane da dama a garin na cigaba da sayen kayan abinci da sauran kayan masarufi suna adanawa tare da yin kaura daga yankunan da ake tsammanin za a kai wa hari.

Ita ma dai gwamnatin Syriar ta kwashe ma'aikata daga hedikwatocin hukumomin tsaro da ke tsakiyar birnin na Damascus.

Rahotanni sun ce an ga motocin sulke da kuma manyan motoci makare da sojoji suna bari unguwar babban filin jirgin Damascus yake inda kuma ake da sansanonin soji har guda uku.

Isra'ila mai makwabtaka da kasar ta Syria ta kakkafa karin naurorin kariya daga makamai masu lizzami kuma ta kirawo karin sojoji daga barikoki domin ko aka yi Syria ta kai mata harin ramuwar gayya idan kawarta Amurka ta kai mata hari.

Karin bayani