Shugaba Mahama zai san makomarsa

Image caption Ana yiwa Ghana kallon abar koyi wajen bin tagfarkin dimokradiyya a Afrika.

Nan da wasu sa'oi ne ake sa ran Kotun Kolin kasar Ghana ta yanke hukunci kan jayyayar da ake game da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi bara.

A yayin zaman sauraron kararraki da bahasi da aka kwashe watanni 8 ana yi, jam'iyyar adawa ta NPP ta ce an tafka magudin da ya isa ya soke bayyana John Mahama a zaman shugaban kasa da hukumar zabe ta yi.

Sai dai jam'iyya mai mulki NDP, ta dage cewar babu isasshiyar madogarar da za ta kai ga soke zaben.

Wannan dai shara'a ce da ba a saba ganin irinta ba a Afrika saboda yadda al'ummar kasar ta Ghana suka rika bibiyarta sau-da-kafa ta gidajen radiyo da talabijin; a gidaje da cikin motoci da kuma a ofisoshinsu, a cewar wani wakilin BBC a Accra.

Shugaba John Mahama da jagoran 'yan hamayya Nana Addo duk sun ce za su amince da hukuncin da kotun za ta yanke a yau. Kusan jami'an tsaro 30,000 ne aka baza a ko'ina a kasar domin tabbatar da tsaro sa'adda kotun ta yanke hukunci.

Karin bayani