'Yan Kenya 41 sun mutu a hadarin mota

Image caption Hadarin mota ba sabon abu bane a Kenya

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce akalla mutane 41 ne suka rasu lokacin da wata motar safa ta kife a garin Narok kusa da Nairobi babban birnin kasar Kenya.

Wani jami'in kula da dokokin hanya, Samuel Kimaru ya ce "lamarin ya yi muni sosai, mutane da dama sun kone".

Motar safa din na kan hanyarta zuwa garin Homa Bay daga Nairobi ne lokacin da ta fada cikin wani rami sannan ta wulwula.

Rahotanni sun nuna cewar hadarin na da nasaba da tukin ganganci na direba da kuma dibar mutane fiye da kima a cikin motar.

Mutane fiye da 2,000 ne suka mutu sakamakon hadarin mota a wannan shekarar a kasar Kenya.

Karin bayani