Ghana: Kotu ta tabbatar da zaben Mahama

Image caption Shugaba Dramani Mahama

Kotun kolin kasar Ghana ta yi watsi da bukatar jam'iyyar adawa ta NPP a kan zaben Shugaba John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC.

An shafe watanni takwas ana shari'ar bayan da 'yan adawa ke zargin cewar an tafka magudi a zaben da aka sanar da Shugaba Mahama a matsayin wanda ya lashe a watan Disambar bara.

Wannan dai shari'a ce da ba a saba ganin irinta ba a Afrika saboda yadda al'ummar kasar ta Ghana suka rika bibiyarta sau-da-kafa ta gidajen radiyo da talabijin; a gidaje da cikin motoci da kuma a ofisoshinsu, a cewar wani wakilin BBC a Accra.

Dan hamayya na jam'iyyar NPP, Nana Addo ya ce zai amince da hukuncin da kotun za ta yanke.

Kusan jami'an tsaro 30,000 ne aka baza a ko'ina a kasar domin tabbatar da tsaro sa'adda kotun ta yanke hukunci.

Karin bayani