Yadda za a rage yaduwar cutar malaria

Image caption Cizon sauro na hallaka dubban mutane a duniya

Wani sabon rahoto ya ce sanya magungunan kashe kwari inda sauro ke kyankyasa, zai iya rage yaduwar cutar zazzabin cizon sauro a yankin Afirka da kuma Asia.

Masu bincike a makarantar koyan aikin likita da kuma ayyukan tsafta wato London School of Hygiene da Tropical Medicine sun ce yayinda sauro ke bijirewa magungunan kashe kwari, ana bukatar sabbin dabarun shawo kan cutar zazzabin cizon sauron, da suka hada da share yankunan da ruwa ke taruwa, inda sauro ke kyankyasa .

Sai dai hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa ba za a iya gabatar da shawarar bin wannan hanya ba a kowanne irin yanayi, kuma ta ce dole ne ayi amfani da wannan hanyar hade da saka magungunan kashe kwari da kuma gidajen sauro.

Mutane fiye da dubu dari shida ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro a shekara ta 2010, galibinsu kuma kananan yara ne a nahiyar Afirka.

Karin bayani