Sake shari'ar likitan Bin Laden a Pakistan

Image caption Dr Shakil Afridi

Wani jami'in shara'a a Pakistan ya janye hukuncin da aka yanke wa Shakil Afridi, likitan da ya taimakawa hukumar leken asirin Amurka ta CIA neman Osama Bin Laden.

An yanke wa Dr Afridi hukuncin daurin shekaru fiye da 30 a gidan yari a kan tuhumar da ta hada da kasancewa da alaka da wata kungiyar 'yan gwagwarmaya da aka haramta.

Ana tsare dashi a wani gidan kaso na birnin Peshawar dake arewa maso yammacin kasar.

Jami'in Sahibzada Mohammed Anees, ya bayar da umurnin sake shara'ar, yana mai cewar alkalin farko ya zarta huruminsa.

Karin bayani