Podolski zai yi jinyar makwanni 10

Image caption Lukas Podolski

Dan kwallon Arsenal, Lukas Podolski zai yi jinyar makwanni takwas zuwa goma saboda raunin da ya ji a wasansu da Fenerbahce.

Da farko an zaci dan kwallon Jamus din zai yi jinyar makwanni uku ne kawai.

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce" abun takaici rauninsa mai tsanani ne".

Jack Wilshere da Aaron Ramsey suma sun samu targade a wasan, amma Wenger ya ce dasu za a kara wasan da Arsenal za ta dauki bakuncin Tottenham a ranar Lahadi.

'Yan wasan Arsenal da a yanzu haka suke fama da rauni su hada da Mikel Arteta, Alex Oxlade-Chamberlain da kuma Thomas Vermaelen.

Karin bayani