Majalisa ta ce Suntai ya koma asibiti

Image caption Gwamna Danbaba Suntai

Majalisar dokoki ta jihar Taraba a Najeriya ta yanke shawarar cewa Gwamna Danbaba Suntai wanda ke fama da rashin lafiya ya koma ya ci gaba da jinya a asibiti, shi kuma mukaddashin Gwamna, Alhaji Garba Umar ya ci gaba da jan ragamar jihar.

Shugaban Majalisar dokokin jihar Haruna Tsokwa, ne ya sanarda haka a taron manema labarai a Jalingo babban birnin Jihar.

Matakin majalisar ya biyo bayan ziyarar da suka kaiwa gwamna Suntai a ranar Laraba don duba yanayin lafiyarsa.

Batun wanda zai jagoranci jihar ya janyo rarrabuwa kawuna a jihar Taraba wacce ke fama da matsaloli masu nasaba da addinni da kabilanci.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum zargin cewar uwargidan gwamnan, Hauwa ce ke kokarin tabbatar da cewar mulki bai subuce musu ba, duk da cewar alamu sun tabbatar da maigidanta baida cikkakkiyar lafiya da zai mulki jama'a.

Karin bayani