Suntai ya yi 'magana' a faifan bidiyo

Image caption A yau ne dai majalisar dokokin jahar za ta yi nazari kan hoton bidiyon.

Mukarraban Gwamna Danbaba Suntai sun fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna shi yana yiwa jama'ar jahar godiya kan addu'oin da suka yi ta yi masa lokacinda yake jinya.

Sai dai tuni wasu jama'a jahar suka nuna shakku kan sahihancin hoton bidiyon, wanda kuma ya nuna wani da aka ce shi ne sabon sakataren gwamnatin jahar a tsaye yana shan rantsuwar kama aiki a gaban gwamnan wanda ke zaune kan kujera.

'' Faifan bidiyon babu murya a wurare da dama sai dai ana iya ganin bakin gwamnan na motsi. Sannan akwai alamun yankewa da hadawa a hoton bidiyon'' In ji wakilin BBC a jahar ta Taraba wanda ya ga wannan faifan bidiyon.

'' Mutum idan ya lura; mutumin da ke magana wanda aka ce shi ne gwamnan bai da kuzari kuma yana numfashi sama-sama sannan muryarsa ba ta fita sosai '', cewar Ishaq Khalid.

Karin bayani