Jama'a na kaura daga Syria

Syria
Image caption Abinci ya soma karanci a Syria saboda fargaba

A babban birnin Damascus na Syria yiwuwar daukar matakin soji na ci gaba da janyo fargaba.

An ruwaito cewa manyan Komandojin soji sun bada umarnin a kwashe dukkanin jami'ai daga mahimman cibiyoyi a wuraren babban birninn Kasar.

Ana kuma samu dogayen layukan motoci makare da akwatuna suna jiran su tsallaka cikin Kasar Labanon.

Kamar yadda wani jam'in tsaron Labanon ya ce akalla mutane dubu shida ne suka tsere kan iyakar a sa'oi 24n da suka gabata.

Magidanta a birnin Damascus sun fadawa BBC cewa akwai karuwar karancin abinci da kuma biredi.

Karin bayani