Rasha ta kira taron gaggawa a kan Syria

Ban Ki-moon
Image caption Ban Ki-moon

Kasashe masu kujerar dindindin a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya sun yi wani taron gaggawa bisa bukatar Rasha domin tattauna batun rikicin Syria, wanda shi ne irinsa na biyu a cikin kwanaki da dama.

Sai dai wasu majiyoyin diflomasiyya sun ce bakin Amurka da Burtaniya da kuma Faransa, wadanda ke son a dauki matakin soja a kan gwamnatin Bashar al Assad, bai zo daya da na Rasha da kuma China ba, wadanda ke adawa da irin wannan mataki.

Kasashen yammacin duniya dai na son a dauki matakin soji a kan gwamnatin Syria ne sakamakon wani hari da makamai masu guba da suke zargi gwamnatin Syriar ta kai a kan unguwannin bayan birnin Damascus.

A ranar asabar ce aka shirya tawagar sufetocin makamai ta majalisar dinkin duniya dake binciken harin na makon jiya za ta bar Syria, to amma jami'ai sunce za ta iya daukar dogon lokaci kafin ta gwada dukanin shaidun da suka tattara.

Sakatare Janar na MDD Ban Ki Moon na sa ran samun sakamakon farko na bayanin baka kan sakamakon binciken su a cikin karshen mako.

Karin bayani