Wakaso zai koma Rubin Kazan

Image caption Mubarak Wakaso

Dan kwallo Ghana Mubarak Wakaso na gabda koma wa kungiyar kwallon kafa ta Rubin Kazan daga Espanyol.

Ana ganin cewar Rubin Kazan za ta biya dalar Amurka miliyon 8 a kan dan kwallon.

Dan wasan mai shekaru 23 ya koma Espanyol daga Villarreal ne a kakar wasan data wuce.

Sanarwar da Espanyol ta fitar, ta ce "Espanyol da Rubin Kazan sun cimma yarjejeniya a ranar Laraba don Mubarak Wakaso ya koma taka leda a Rasha, idan har aka gwada lafiyarsa".

A wasansa a Espanyol, Wakaso ya fuskanci matsaloli inda sau biyu ana bashi jan kati.