Kotu ta saki kakakin Laurent Gbagbo

Tsohon kakakin Laurent Gbagbo, Justin Katinaan
Image caption Justin Kone ya yi fatan abin da ya faru a gare shi ya samu maigidansa

Wata kotun majistire a Ghana, ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake wa tsohon kakakin hambararren shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo.

Kotun ta ce tuhumar da ake wa Justin Kone Katinaan na da nasaba da siyasa, kuma masu gabatar da kara sun kasa kawo kwararar hujjoji.

An kama kakakin bara a Ghana, inda aka tuhume shi da aikata laifuka goma, da suka hada da fashin kudi da yawansu ya kai dala miliyan 640 a kasarsa.

Justin ya yi murna da hukuncin kotun, sai dai ya ce yana tunanin ubangidansa da ke daure.