Faransa na goyon bayan hari a kan Syria

Image caption Faransa da Jamus sun rabu a kan Syria

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ce kasarsa na kan bakarta na kokarin ganin an dauki mataki a kan Syria duk da cewar 'yan majalisar dokokin Birtaniya sun ki amincewa da batun daukar matakin soji.

Mista Hollande ya ce suna duba yiwuwar amfani da duk wani zabi da suke dashi, kuma ba za a janye batun soma kaddamar da luguden wuta ba a cikin 'yan kwanaki.

Kalamansa na zuwa ne bayan da Sakataren tsaron Amurka, Chuck Hagel yace Washington za ta ci gaba da neman goyon bayan kawayenta a kokarin daukar matakin soji.

Amurka ta zargi gwamnatin Syria da yin amfani da makamai masu guba amma Shugaba Assad ya musanta.

Sai dai kuma Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle ya ce kasarsa ba za ta sa hannu wajen amfani da karfin soji a kan Syria ba.

A halin yanzu dai masu bincike na majalisar dinkin duniya a kan batun amfani da makami mai guba a Syria a karshen wannan makon za su mika rahoton su ga Sakatare Janar, Ban Ki Moon a kan abinda suka gani.