An ajiye kan mutum a ofishin 'yan sanda

Shugaban hukumar 'yan sandan Kenya, Johnstone Kavuludi
Image caption 'Yan sanda sunce sun dauki wannan lamari a matsayin barazanar kisa

Rundunar 'yan sandan Kenya na bincike game da kan mutum, da aka ajiye a kofar ofishin shugaban hukumar 'yan sandan kasar, Johnstone Kavuludi a Nairobi.

Akwatin da aka sanya a leda ruwan dorawa, na kuma dauke da hannaye biyu na mutum, dukansu a cikin jini.

Haka kuma an bar wani sako makale a jikin akwatin, inda aka rubuta cewa " Kavuludi saura kai."

Tun bayan rantsar da Mr. Kavuludi a bara, yake ta yunkurin yin garambawul ga rundunar 'yan sandan kasar, wacce aka ce ta fi kowacce fama da cin hanci da rashawa a gabashin Afrika.