Makafi na kokawa a Najeriya

Image caption Makafi na kokawa a Najeriya

A Najeriya, kungiyar makafi reshen arewacin kasar ta koka game da abin da ta kira muzgunawa 'ya'yanta da hukumomin babban birnin tarayya Abuja ke yi musu.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin kasar da ta cika alkawukan da ta dauka na samarwa nakasassu tallafin kudade don yin wasu sana'o'i wanda zai basu damar dogaro da kansu maimakon barace-barace.

Sakataren yada labarai na kungiyar Malam Muntari Saleh ya ce kamasun tamkar hana su walwala ne.

Kungiyar makafin dai sun yi barazanar yin zaman durshen a babban birnin Tarayya Abuja matsawar aka ci gaba da kama mabobinsu.

Karin bayani